Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na hurriyet cewa, za a fara watsa wani fim da aka hada kan addinin Musulunci da tarihinsa a tashar talabijin ta ZDF ta kasar Jamus, wanda ya hada da bayanai kan wurare masu tsarki na musulmi a kasashe daban-daban.
Rahoton ya ce wannan silsilar fim na dauke da bayanai dangane da matsayin addinin Musulunci kan lamurra da dama, da suka hada da matsayinsa kan shari'a jihadi, tarihin safkar kur'ani da matsayin kur'ani da dai sauran batutuwa masu kama da hakan.
Matakin gwamnatin Jamus ta dauka na girmamam mutumin da ya ci zarafin addinin Musulunci ya harzuka musulmin kasar Jamus da ma na dniya baki daya.
655372