Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habrta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na jaridar financil times cewa, a kasar Birtaniya ne za a fara gudanar da wani zaman taron kara wa juna sani kan harkokin kudi a mahangar addinin muslunci a birnin London fadar mulkin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa, zaman taron zai samu halartar wakilai na cibiyoyin kudi da harkokin kasuwanci na musulmi sama da 500, kamar yadda kuma wasu daga cikin cibiyoyin kasuwanci na kasar Birtaniya da wasu kasashen za su halarci zaman taron.
Tron zai mayar da hanakali ne kan batutuwa da suka danganci bunkasa harkokin tattalin arziki da kasuwanci a mahangar addinin Musulunci.
655498