IQNA

Musulmin Nigeria Sun Nuna Rashin Amincewa Da Wulakanta Kur'ani

12:06 - September 19, 2010
Lambar Labari: 1996763
Bangaren siyasa da zamnatakewa; Bayan fitar da bayanin jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Ozma Sayyid Khamene'i, musulmin Nigeria sun matukar damuwarsu kan tozarta addinin Musulunci ta hanyar kone kur'ani.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na bangaren hulda da jama'a na cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilmi cewa, bayan fitar da bayanin jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Ozma Sayyid Khamene'i, musulmin Nigeria sun matukar damuwarsu kan tozarta addinin Musulunci ta hanyar kone kur'ani da wasu suka yi a kasar Amurka.

Bayanin ya ce bisa la'akari da cewa mutanen Nigeria akasarin musulmi ne masu riko da kur'ani tare da ganin girmansa, sun mayar da martani ta hanyar yin Allawadai da duk wani mataki na keta alfarmar kur'ani mai tsarki.

A nasa bangaren shugaban kasar Nigeria Good Luck Jonathon, duk kuwa da kasantuwarsa kirista, ya yi Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansu kirista suka yi a Amurka.

656988



captcha