Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar yaum sabi ta kasar Masar an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da zaman tattaunawar addinai a kasar Japan a yau tare da halartar wakilan kasashen duniya da dama da suka hada da na musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa Ibrahim Najm daya daga cikin mambobin tawagar kasar Masar a taron kuma dan majalisar dokokin, shi ne zai fara gudanar da jawabi, daga bisani kuma za a bayar da dama ga sauran wakilai.
Babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce karfafa dukkanin mabiya addinai da su zama masu fahimtar juna da girmama akidun juna baki daya, ta yadda za a samu zaman lafiya mai dorewa a duniya.
658176