IQNA

Gangamin Lauyoyin Masar Kan Nuna Rashin Amincewa Da Kone Kur'ani

17:31 - September 22, 2010
Lambar Labari: 1999679
Bangaren kasa da kasa; Wasu daga cikin lauyoyin kasar Masar sun gudanar da wani gangami, domin kalubalantar masu kiyayya da Musulunci da suka kone kur'ani mai tsarki a 'yan kwankin da suka gabata.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar kasar Masar Yaum sabi ta bayar da rahoton da ke cewa, Wasu daga cikin lauyoyin kasar Masar sun gudanar da wani gangami, domin kalubalantar masu kiyayya da Musulunci da suka kone kur'ani mai tsarki a 'yan kwankin da suka gabata a kasar Amurka.

Lauyoyin da suka gudanar da gangamin sun yi ta rera taken nuna rashn amincewa da matakin da Terry Jones ya dauka na ayyana ranar 11 ga watan satumba a matsayin ranar kone kur'ani mai tsarki ta duniya.

Sun bayyana wannan mataki da cewa ya samo asali ne daga irin ta'assubancin da yake fama da shi na kiyayya da Musulunci, wanda hakan bai kara wa Musulunci da kur'ani komai ba illa daukaka.

660055




captcha