Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Aldastur ta kasar Jordan an bayyana cewa, babbar cibiyar kula da harkokin fikihun muslunci ta fitar da wani bayani da ke yi kakakusar suka kan wani malamin addinin kirista a kasar Masar da ya ci zarafin kur'ani mai tsarki a cikin 'yan makonnin da suka gabata.
Bayanin ya ce kiran da malamin kiristan ya yi wanda shi ne mutum na biyu a majami'ar kiristocin Masar, kan cewa a cire wasu daga cikin ayoyin kur'ani babban wukanci ne ga addinin muslunci da musulmi.
A kan bayanin malaman wannan cibiya yana yin Allawadai da kakausar murya kan wannan furuci, kuma ya neman wannan mutum da ya nemi gafarar dukkanin al'ummar musulmi na duniya.
666477