IQNA

Komitin Koli Na Musulmi A Aljeriya Ya Yi Allah Wadai Da Watsa Littafin Zanen Batanci

11:31 - October 05, 2010
Lambar Labari: 2006879
Bangaren kasa da kasa:komitin kolin Musulunci a Aljeriya HCI a jiya ne sha daya ga watan Muhr ya yi Allah wadai da yadda aka watsa littafin tugyan Sukut day a kumshi zane-zanen batanci kan ma'aikin Allah annabin tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da aka yi a kasar Denemark.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci bayan ya nakalto daga kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa AFP ya watsa wannan bayanin da cewa; komitin kolin Musulunci a Aljeriya HCI a jiya ne sha daya ga watan Muhr ya yi Allah wadai da yadda aka watsa littafin tugyan Sukut day a kumshi zane-zanen batanci kan ma'aikin Allah annabin tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da aka yi a kasar Denemark. Sanarwar ta nuna cewa wannna wani mataki ne da ke nuna yadda makiya ke neman haddasa tashin hankali da tashina-tashina tsakanin mabiya addinai a duniya.

668131
captcha