IQNA

An Nuna Zanen Yadda Masallaci Da Cibiyar Musulunci Ta New York Za Su Kasance

11:29 - October 05, 2010
Lambar Labari: 2006882
Bangaren kasa da kasa; An nuna zanen da aka bada shawara kansa na gina masallaci da cibiyar Musulunci a tsakiyar birnin New Yurk na kasar Amerika a kusa da tagwayen benaye da aka kai wa harin ta'addancin ranar sha daya ga watan Satumba.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Examiner ta watsa rahoton cewa; An nuna zanen da aka bada shawara kansa na gina masallaci da cibiyar Musulunci a tsakiyar birnin New Yurk na kasar Amerika a kusa da tagwayen benaye da aka kai wa harin ta'addancin ranar sha daya ga watan Satumba. Taswira goda uku ne kamfanin Soma da aka daurawa nauyin tsarawa ya nunawa jama'a.Taswirar ta kumshi taswira ta ciki ta cibiyar musuluncin mai hawa sha shida da ta kumshin tsarin gini na Musulunci da kuma na birnin New York kuma wannan shi ne karon farko.


668250
captcha