Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da zaman taron ministocin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi a birnin Kualalampour na kasar Malazia tare da halartar wasu daga cikin masana daga sassa daban-daban na duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Bernama cewa, za a gudanar da zaman taron ministocin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi a birnin Kualalampour na kasar Malazia tare da halartar wasu daga cikin masana daga sassa daban-daban.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na biyar da za a gudanar da wannan zaman taro wanda kungiyar kula da ayyukan al'adu da ilimi ta kasashen musulmi ta ISESCO ta kan shirya shekara-shekara.
Wannan zaman taro dai zai yi dubi ne kan muhimman batutuwa da suka danganci harkokin ilimi a kasashen musulmi da kuma hanyoyin da za a bi a kara habbaka su da mayar da nasu na zaman.
671224