.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar watsa labarai ta OCI ya watsa rahoton cewa; kungiyar kare hadin kan kasashen musulmi ta yaba da amincewa da matakin da hukumar hadin kan kasa da kasa ta dauka na aiyana makon guda a cikin eatan Fevreru na kowace shekara a matsayin makon tuntubar juna tsakanin addinai na duniya.Sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ikmalul Dine Ihsan Uglu ya fitar da wanna bayani a ranar sha daya ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara ya jinjina da yabawa wannan mataki.
687889