Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; ofishin darektan kula da harkokin al'adu da dangantaka ta Musulunci a lokacin bukin kaddamar da yaruka guda biyu na Kazaki da Miyamari a kamfanin yada labarai na Ikna ya bayyana cewa; yin hidima ga kur'ani wani abin iftikhari ne ga hukumar al'adu da dangantaka ta Musulunci.Muhsin Pak Ayin mukaddashin wannan hukumar ta al'adu a yau ashirin da hudu ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara rana ce mai muhimmanci domin a wannan rana ce muke kaddamar da yaruka biyu na Kazaki.
696172