Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Al'alam ya watsa rahoton cewa; kungiyoyin Palasdinu a daidai wannan lokaci na shagulgulan babbar salla sun bukaci hadin kan muslmi da larabawa domin taimakawa al'amarin Palasdinu da Kudus mai tsarki.Har ila yau Aiman Taha daya daga cikin shugabanni da jagororin kungiyar gwagwarmaya Palasdinu ta Hamas dangane da wannan labari ya bayyana cewa; hadewar musulmi daga ko ina na duniya a wanna fili na Arafa wannan na nuni da cewa musulmi na iya hada kansu domin kare kansu daga makiya.
696981