Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta gidan talbijin din labarai ta Najaf Ashrafya watsa rahoton cewa; Gasar fahimtar kur'ani mai girma ga yara kanana yan makaranta a Iraki a bangarori daban –daban da aka fara tun ranar ashirin da takwas ga watan Aban da muke ciki na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin Najaf mai tsarki. Kuma wannan gasar mu'assisar Shahid Mihrab net a dauki nauyin gudanarwa da zummar karawa yara kananan yan makaranta karfin guiwa da himma ta fuskar fahimtar kur'ani mai girma.
697898