Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta ajmf ya watsa rahoton cewa; a ranar talata wato gob eke nan biyu ga watan Azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin Kurbi na Isun na kasar ta Faransa za a gudanar da taron tattauna kan abubuwa masu kima da daraja na addinan Ibrahima a tsawon tarihi.Wannan taro kungiyar abukkan juna a Musulunci da yahudawan Faransa AJMF tare halartar wakilan addinin Musulunci na na kiristoci da yahudanci.Gudanar da irin wannan taro nada matukar muhimmanci matuka gaya da kuma zai kara samar da hadin kai a tsakanin mabiya addinan manya guda uku na duniya.
698991