Bangaren kasa da kasa, Ministan ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci a kasar Indonsia ya bayyana cewa, kasarsa na yi iyakacin kokarinta domin yin nazari tare da sauran kasashe da ba na musulmi ba kan koyarwa addinin muslunci da akidojinsa domin wayar da kansu kan addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafion sadarwa na Bernama na kasar Malazia cewa, ministan ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci a kasar Indonsia ya bayyana cewa, kasarsa na yi iyakacin kokarinta domin yin nazari tare da sauran kasashe da ba na musulmi ba kan koyarwa addinin muslunci da akidojinsa domin wayar da kansu kan addinin muslunci da koyarwarsa.
Bayanin ya ci gaba da cewa ministan ya jadda muhimmancin yin hakan, domin a cewarsa rashin yin bayanin addinin muslunci ga sauran al'aummomin kan sanya su zama cikin jahilcinsa da kuma amincewa da abin da wasu kan fadi kan kansa na bakantawa.
Ya ce daga cikin kasashen da suke yin nazari tare dad a su akwai kasashen Rasha, Thailanda, Barma, Viatnam da dai sauransu, wanda a cewarsa hakan ya yi gagarumin tasiri wajen wayar da kansu.
704693