Bangaren kasa da kasa, An bude wani baje koli na kayayyakin Ashura a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, wanda ke samun karbuwa daga al'ummar musulmi na kasar musamman ma mazauna birnin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na masallacin Zainabiyya cewa, an bude wani baje koli na kayayyakin Ashura a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, wanda ke samun karbuwa daga al'ummar musulmi na kasar musamman ma mazauna birnin na Istanbul.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje koli shi ne irinsa na farko da aka gudanar a babbar cibiyar baje kayayyakin al'adu da ke cikin birnin Istanbul, wanda mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah na kasar suka dauki nauyin shiryawa, da nufin kara wayar da musulmi kan muhimmancin Ashura.
Daruruwan mutanen ne suka hallara a lokacin da aka bude wannan gagarumin baje koli na Ashura a birnin Istanbul, wanda ya hada da hotuna da zane-zanen abubuwan da suka faru a karbala a ranar Ashura.
705610