Bangaren kasa da kasa da kasa, Wata cibiyar kiwon lafiya da ke birnin Frankfort a kasar Jamus, ta kirayi wani likita da aiki a karkashinta tare da jankunnensa, bayan da ya ki amincewa ya karbi wata maras lafiya musulma da take sanye da hijabin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Two Circles na yanar gizo an bayyana cewa, wata cibiyar kiwon lafiya da ke birnin Frankfort a kasar Jamus, ta kirayi wani likita da aiki a karkashinta tare da jankunnensa, bayan da ya ki amincewa ya karbi wata maras lafiya musulma da take sanye da hijabin muslunci da wasu suke kyama a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa musulman kasar Jamus suna fuskantar matsalar kyama da nuna musu wariya baro-baro daga gwamnati da cibiyoyi da kuma al'ummar kasar, wadanda akasarinsu mabiya addinin kirista ne. Wannan cibiya ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa ba a nuna banbnci a cikin ayyukanta.
Rahoton ya ce wannan jan kunne zai yi tasiri wajen taka birki ga wasu likitoci da wata kila suke da niyar daukar wasu matakan makamantan hakan da suke aiki karkashin wannan cibiya.
705534