Bangaren kasa da kasa, Za a kamala taron kasa da kasa da ake gudanarwa kasar Cyprus ta arewa da ke karkashin ikon Turkiya, dake yin bahasi kan al'adun muslunci da ci gabansu a tarihin duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, Za a kamala taron kasa da kasa da ake gudanarwa kasar Cyprus ta arewa da ke karkashin ikon Turkiya, dake yin bahasi kan al'adun muslunci da ci gabansu a tarihin duniya, da ke samun halartar masana da malama jami'oi daga sassa daban-daban na duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa bangaren kula da bunkasa harkokin al'adu da ilimi na kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC ne ya dauki nauyin shirya gudanar da zaman taron, da nufin kara wayar da kan al'ummomin duniya musamman ma masu bincike kan mtsayin al'adun muslunci a tarihi.
A yau ne za a kawo karshen zaman taron wanda aka yi wa take da taron ci gaban al'adun muslunci na Medtarania a matsayi na kasa da kasa.
705563