Bnagaren kasa da kasa, Ministan harkokin cikin gida na kasar Jamus zai gudanar da wata ganawa tare da wakilan kungiyoyi da cibiyoyin musulmi na kasar, a ranar Laraba mai zuwa a birnin Bonn na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an hurriyat an bayyan cewa, ministan harkokin cikin gida na kasar Jamus zai gudanar da wata ganawa tare da wakilan kungiyoyi da cibiyoyin musulmi na kasar, a ranar Laraba mai zuwa a birnin Bonn na kasar ta Jamus.
An watsa wannan rahoto bayan da ma'ikatar harkokin cikin gida ta kasar Jamus ta tabbatar da hakan a cikin wani bayani da ta fitar, inda ta bayyana cewa ministan zai gana da limaman masallatan juma'a da kuma shugabannin kungiyoyi da cibiyoyin musulmin kasar.
Jamus dai na daya daga cikin kasashen turai da musulmi suke fuskantar matsaloli da dama saboda akidarsu ta bin koyarwar addinin muslunci, inda ake nuna musu wariya da kyama kai tsaye, daga mataki na zamantakewa har zuwa mataki na gwamnati.
705943