Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na 12imam an bayyana cewa, ana gudanar da taron addu'ar mai babban matsayi du'aul Komail a babbar cibiyar nan ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da ke birnin Geneva fadar mulkin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro da aka saba gudanarwa yana samun halartar musulmi daga sassa daban-daban na kasar, wanda hakan nuni da irin gagarumin ci gaba da musulmi suke samu a kasar wajen gudanar da tarukansu addini.
Taron dai bai takaitu da karatun addu'ar ba, har aka gabatar da jawabai na fadakarwa ga musulmi kan addininsu da yadda ya kamata su yi riko da koyarwasa a cikin dukkanin sassa na rayuwar yau da kullum.
706807