Bangaren kasa da kasa, An saka bakaken tutoci a kan hasumiyoyin hubbaren Imam Hussain (AS) da kuma hubbaren Abul fasl Abbas (AS) dake garin Karbala mai alfarma, domin fara gudanar shirye-shiryen tarukan Ashura.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun an bayyana cewa, an saka bakaken tutoci a kan hasumiyoyin hubbaren Imam Hussain (AS) da kuma hubbaren Abul fasl Abbas (AS) dake garin Karbala mai alfarma, domin fara gudanar shirye-shiryen tarukan Ashura a cikin wannan wata na muharram.
Bayanin ya ci gaba da cewa tarukan ashura da aka saba gudanarwa a kasar Iraki, na samun halartar miliyoyin mutane daga sassa daba-daban na duniya, musamamn ma daga kasashen musulmi, inda mabiya tafarkin iayalan gidan manzon kan mayar da hankali wajen raya wadannan ranaku masu albarka.
Yanzu haka dai dubban mutane daga kasashen duniya sun fara isa kasar Iraki da nufin halartar tarukan na Ashura da za a fara gudanarwa a cikin wannan mako da muke ciki.
707470