Bangaren kasa da kasa, Za a bude tashar talabijin ta farko ta Musulunci mai suna Hejrat a kasar Malazia, inda za a gudanar da taro a hukumance a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar, tare da halartar fraministan kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama cewa, za a bude tashar talabijin ta farko ta Musulunci mai suna Hejrat a kasar Malazia, inda za a gudanar da taro a hukumance a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar, tare da halartar fraministan kasar Najib Razzaq.
Bayanin ya ci gaba da cewa taron bude wannan tasha zai samu halartar wasu daga cikin malaman addinin muslunci da kuma wakilan cibiyoyi da kungiyoyin muslunci na kasar, haka nan kuma taron zai samu halartar sheikh Muhammad Abdulaziz, babban sakataren cibiyar bunkasa ayyukan addinin muslunci a kasar.
Babbar manufar bude wannan tasha dai ita ce kara bunkasa harkokin addinin muslunci da kuma fahimtarsa a tsakanin al'ummonin kasar, wadanda akasarins mabiya addinin muslunci ne.
708220