IQNA

Musulmin Faransa Sun Kafa Wani Babban Tanti Na Taimaka Ma Mutane

10:49 - December 09, 2010
Lambar Labari: 2044849
Bangaren kasa da kasa, Babban masallacin birnin Paris fadar mulkin kasar Farnasa ya kafa wani babban tanti na taimaka ma mutane a kamar yadda ya saba a kowane lokacin sanyi, musamamn ma ga mutanen da ba su da gidaje ko wata mafaka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na mosque-e-paris cewa, babban masallacin birnin Paris fadar mulkin kasar Farnasa ya kafa wani babban tanti na taimaka ma mutane a kamar yadda ya saba a kowane lokacin sanyi, musamamn ma ga mutanen da ba su da gidaje ko wata mafaka a birnin.

Wannan shi ne karo na 24 da bababn masallacin paris yake gudanar da irin wannan shiri, inda ya kan samar da abubuwan bukata musamman ma alokacin sanyi, domin taimaka ma mutanen da ba su da galihu suke gararamba akan tituna.

Mutane kan amshi abinci da abin sha daga wannan babban tanti, babbar manufar yin hakan dai ita ce nuna kyawawan dabiu na musulmi da kuma kyakkyawar koyarwar Musulunci ga mabiya addinin muslunci.

709188


captcha