Bangaren kur'ani, An sanar da sunayen alkalan da za su gudanar da alkalanci a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da ta kebanci daliban jami'a musulmi da za a gudanar a birnin Mashad mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da babban sakataren kwamitin zabar alkalan gasar kur'ani ta kasa da kasa Isa Alizadeh ya bayyana cewa, an sanar da sunayen alkalan da za su gudanar da alkalanci a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da ta kebanci daliban jami'a musulmi da za a gudanar a birnin Mashad.
A cikin zantawar ya tabbatar da cewa tuni an riga an zabi tare da sanar da sunayen alkalan da za su gudanar da alkalanci a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da ta kebanci daliban jami'a musulmi da za a gudanar a birnin Mashad da ke lardin Khurasan a jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Alkalan dai za su taka rawa wajen ganin an gudanar da gasar kamar yadda ya kamata, tare da kiyaye dukkanin hakkokin na masu gudanar da gasar a dukkanin bangarorinta.
710995