Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga jaridar Al'anbiya da ake buga ta a kasar ta Koweiti ya watsa rahoton cewa; a karon farko za a gudanar da taron kasa da kasa kan Kur'ani mai girma a kasar Koweiti da aka bawa taron sunan ci gaba ta fuskar harda da koyar da karatun Kur'ani mai girma mai taken bada gudummuwa a yin hidima ga Kur'ni. Adil Alfalah mukaddashin ministan da ke kula da harkokin addini a kasar ta Koweiti dangane da wannan labari ya bayyana cewa; Taron da za a bude a ranar ashirin da tara ga watan azar dangane da Kur'ani mai girma da ofishinm kula da harkokin kur'ani mai girma ya shirya da ke karkashin ma'aikatar harkokin addini ta kasar ta Koweiti za a gudanar ne a babban masallaci na wannan kasa. Kuma za a samu halartar makaranta kur'ani fitattu masu yawa daga duniyar musulmi da za su halarci wannan taro.
713221