Bangaren kasa da kasa, Dubban mutane ne suke ci gaba da gudanar zanga-zangar nuna rashin amince da dokar hana saka hijabin musulunci a makarantun kasar Azarbaijan, wadda wasu daga cikin majalisar dokokin kasar suka bijiro da ita.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga wasu majiyoyi daga birnin Baku fadar mulkin kasar Azarbaijan cewa, dubban mutane ne suke ci gaba da gudanar zanga-zangar nuna rashin amince da dokar hana saka hijabin musulunci a makarantun kasar Azarbaijan, wadda wasu daga cikin majalisar dokokin kasar suka bijiro da ita kuma ma'aikatar ilmin kasar ta sanar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da daya daga cikin masu gudanar da zanga-zangar ya bayyana cewa, suna nuna rashin gamsuwarsu da dokar take hakkin dan adam da aka sanar da hana mata saka hijabin muslunci a makarantu.
Masu gangamin sun mika wata wasika zuwa ga ministan ilimi da suka taru a gaban ofishinsa, da ke neman ya gaggauta janye wannan dokar da yanar tun ba aje ko'ina ba.
713317