Bangaren kasa da kasa, Malazia ta gabatar da wata shawar ta gudanar da gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da nufin karfafa tattaunawa tsakanin bangarorin musulmi da warware abubuwan da aka yi sabani a kan su.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama cewa, malazia ta gabatar da wata shawar ta gudanar da gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da nufin karfafa tattaunawa tsakanin bangarorin musulmi da warware abubuwan da aka yi sabani a kan sun a ilimi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar kur'ani za ta zama irinta ce ta farko da za a gudanar, kuma za a ci gaba da gudanar da ita a kowace a kasashen musulmi daban-daban inda makafi za su samu damar nuna basirar da Allah ya basu ta fuskr karatu da hardar kur'ani.
Yanzu haka dai kasashen musulmi suna ci gaba da yin nazari kan wannan shawara ta Malazia, kuma ga dukkan alamu kasashen za su amince da wannan shawara.
713814