Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da zaman taro na kwamitin sadarwa da ya kunshi kafofin yada labarai nagidajen radiyo na kasashen musulmi a karon farko a birnin Jidda na kasar saudiyya, tare da halartar mambobin kwamitin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar Yeman saba an bayyana cewa, za a gudanar da zaman taro na kwamitin sadarwa da ya kunshi kafofin yada labarai nagidajen radiyo na kasashen musulmi a karon farko a birnin Jidda na kasar saudiyya, tare da halartar mambobin kwamitin dake kasashen duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai mayar da hankali kan irin muhimman ayyukan da suke gaban kafofin sadarwa na kasashen musulmi, musamman ma a wannan lokaci da ae da matukar bukatuwa zuwa kara wayar da kan al'ummomin duniya dangane da addinin muslunci.
Ya ce yanzu haka dai an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanr da wannan zaman taro, wanda ake sa ran zai samu halartar manyan jami'ai a fuskar sadarwa daga kasashen musulmi.
715082