Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da babban taro wanda shi ne irinsa na farko na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Masar, wanda zai gudana a birnin alkahira fadar mulkin kasar tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da kuma kashen duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar alkauthar an bayyana cewa, za a gudanar da babban taro wanda shi ne irinsa na farko na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Masar, wanda zai gudana a birnin alkahira fadar mulkin kasar tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da kuma kashen waje.
Rahoton ya kara da cewa wannan zama zai mayar da hanakali kan muhimmancin da ke tatatre da samun hadin kai mai dorewa tsakanin dukkanin bangarorin musulmi, wanda hakan zai bayar da damar warware matsaloli da dama da ke kawo rashin fahimta tsakanin juna, musamman kan batun sunna da shi'a.
Gudanar da babban taro wanda shi ne irinsa na farko na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Masar, wanda zai gudana a birnin alkahira fadar mulkin kasar tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da kuma kashen duniya.
717973