Bangaren kasa da kasa, Za a kafa wani kwamitin hadin gwiwa tsakanin mabiya addinin kirista da kuma mabiya addinin Musulunci a kasar Masar da nufin samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinan biyu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muhit an bayyana cewa, za a kafa wani kwamitin hadin gwiwa tsakanin mabiya addinin kirista da kuma mabiya addinin Musulunci a kasar Masar da nufin samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinan biyu da ke zaune a kasar.
Rahoton ya kara da cewa babbar manufar kafa wanna kwamiti ita ce haifar da yanayi na zaman lafiya da kuma kawo karshen tashe-tashen hankula tsakanin mabiya addinan biyu, musamman ma a cikin 'yan lokutanan, lamarin da ya fuskanci Allawadai daga malaman addinin muslunci.
A cikin watan decemban da ya gabata an kai wasu hare-hare kan majami'oin mabiya addinin kirista a Masar, kamar yadda aka kai wasu makamantansu a lokacin da suke bukin sabuwar shekarar bana.
723227