IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Tattaunawa Tsakanin Mabiya Addinan Kiristanci Da Musulunci

16:49 - January 09, 2011
Lambar Labari: 2061563
Bangaren kasa da kasa, wata tawagar musulmi ta gana da baban malamin addinin kirista na kasar Masar, tawagar wadda ta hada manyan malaman jami’ar Azhar daga ciki kuwa har da babban malamin Azhar din Ahmad Tayyib, da kuma ministan ma’ikatar kula da harkokin addini.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na UOIF cewa, wata bababr tawagar musulmi ta gana da baban malamin addinin kirista na kasar Masar, tawagar wadda ta hada manyan malaman jami’ar Azhar daga ciki kuwa har da babban malamin Azhar din Ahmad Tayyib, da kuma ministan ma’ikatar kula da harkokin addini ta kasar ta Masar, gami da wakilai na kungiyoyin kasashen musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai bayanai da malamai daban-daban suka fitar da ke yin Allawadai da wannan danyen aiki, yayin da wasu suke kallon hakan a matsayin wata makida daga makiya musulunci, inda suke yin hakan domin haifar da rikici tsakanin muslmi da kuma kiristoci musaman ma yahudawan sahyuniya da suke gaba da dukkanin bangarorin biyu.
Tawagar musulmi ta gana da baban malamin addinin kirista na kasar Masar, tawagar wadda ta hada manyan malaman jami’ar Azhar daga ciki kuwa har da babban malamin Azhar din Ahmad Tayyib, da kuma ministan ma’ikatar kula da harkokin addini ta kasar.
726100

captcha