IQNA

16:08 - January 15, 2011
Lambar Labari: 2064799
Bangaren kasa da kasa, Jami’an tsaron kasar Saudiyya na ci gaba da kame mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da suka saka kyallayen Ashura a lokacin da ake shirin gudanar da tarukan tunawa da cika kwanaki arba’in na shahadar Imam Hussain (AS) tare da sahabbansa a Karbala.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rasid an bayyana cewa, jami’an tsaron kasar Saudiyya na ci gaba da kame mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da suka saka kyallayen Ashura a lokacin da ake shirin gudanar da tarukan tunawa da cika kwanaki arba’in na shahadar Imam Hussain (AS) tare da sahabbansa a Karbala kamar yadda suka saba akowace sheakara.
Bayanin ya ci gaba da cewa jami’an ‘yan sanda na gwamnatin Saudiyya suna bi gida-gida suna kame duk wanda ya kasance cikin mabiya mazhabar iayalan gidan manzon Allah da suka gudanar da aikace-aikace a lokacin tarukan Ashura, da kuma wadanda suke gudanar da wasu shirye-shirye na tunawa da arba’in din Ashura.
Gwamnatin wahabiyawan saudiyya ta jima tan adaukar matakan dakile mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah ta hanyoyi da dama, amma hakan bai hana su ci gaba da bin koyarwar manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka ba, duk kuwa irin matsanancin matsin lamba akansu.
Kame mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da suka saka kyallayen Ashura a lokacin da ake shirin gudanar da tarukan tunawa da cika kwanaki arba’in na shahadar Imam Hussain (AS) tare da sahabbansa a Karbala da jami’an tsaron Saudiyya ke yi ba sabon lamari ba ne.
730136
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: