Bangaren kasa da kasa, An gudanar da zaman taro na kara wa juna sani kan rayuwar babban malaimin addinin muslunci marigayi Ayatollah Ozma Sayyid Abul Kasim Alkhu’i a biranan Najaf da kuma Karbala masu alfarma, tare da halartar masana da manyan malaman addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun an bayyana cewa, an gudanar da zaman taro na kara wa juna sani kan rayuwar babban malaimin addinin muslunci marigayi Ayatollah Ozma Sayyid Abul Kasim Alkhu’i a biranan Najaf da kuma Karbala masu alfarma, tare da halartar masana da manyan malaman addinin muslunci gami da malan jami’a.
A ayin gudanar da zaman karawa juna sani kan rayuwar malamin, an gabatar da wani littafi da aka rubuta kan rayursa baki daya, da hada bangaren rayuwarsa ta kuruciya, da kuma rayurwa ta neman ilimi, gami da rayuwarsa ta malamanta, inda ya yi fama da fadi tashi mai yawan gaske a cikin rayuwarsa kafin kaiwa ga babban matsayi na malamin addinin musulunci da ake komawa zuwa gare shi .
Ayatollah Sayyid Kho’i ya kasance babban malamin addinin muslunci na zamaninsa wanda mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah akasarinsu suke komawa zuwa gare shi, ya rubuta tarin littafai na bangarorin ilimi da ba su gushe ba ana amfana da su a sassa na ilimin Hauza da ma jami’oin kasashen musulmi.
730095