Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga shafin sadarwa na yanr gizo na ISESCO cewa, an buga tare da fitar da littafin nazari kan addinin muslunci a cikin kasashen nahiyar turai, wanda cibiyar kula da harkokin muslunci a nahiyar turai tare d ahadin gwiwa da kungiyar bunkasa al’du da ilmin muslunci ta duniya suka dauki nauyin wallafawa tare da fitar da shi.
Wannan littafi ya mayar da hankali a kan yanayin rayuwar musulmi da kuma yanayin ‘yancinsu na addini a cikin kasashen Birtaniya, Faransa, Italia, Jamus da kuma Spain. Babbar manufar hakan ita ce tabbatarwa duniya cewa a cikin wadannan kashe musulmi da suke rayuwa, wasunsu ‘yan asalin kasar ne wasunsu kuma baki ne, wasu kuma baki amma sun riga sun zama ‘yan kasa.
Da dama daga cikin musulmin da suke rayuwa a wasu kasashen yammacin turai suna kokawa dangane d aydda ake nuna musu wariya tare da tsangwama saboda addinisu, hakan kuma ta fara wakan ane bayan bullar wasu kungiyoyi da jam’iyu masu tsananin gaba da addnin musulunci.
Kasashen Holland da Jamus na daga cikin kasashen da ke gaba-gaba wajen nuna wa musulmi matukar kyma da gaba maras misiltuwa, inda a jamus har gwamnati tana girmama mutanen da suka yi suna da gaba da addinin muslunci.
729957