IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Ta Kasa Da Kasa A Qatar

15:15 - January 18, 2011
Lambar Labari: 2066945
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, wadda ma'iakatar kula da ayyukan addinin musulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar na jaridar kasar Qatar ta Al-sharq an bayyana cewa, Za a gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, wadda ma'iakatar kula da ayyukan addinin musulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin watan gobe.

Wadanda suke jagorantar kwamitin zartarwa na shirya gasar sun bayyana cewa an kammala dukkanin shirye-shirye na gdanar da wannan gasa, amma ana ci gaba da yin rijistar sunayen masu gudanar da gasar, kuma zata kebanci matasa ne dab a su wuce shekaru goma sha biyu ba abin da ya yi kasa.

Gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, wadda ma'iakatar kula da ayyukan addinin musulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, zai kara karfafa gwiwar matasa masusha'awar shiga gasar kur'ani.

732068



captcha