IQNA

Tawagar Labanon Ta Halarci Taron Majalisar Dokokin Kasashen Musulmi A Abu Zabin

15:51 - January 19, 2011
Lambar Labari: 2067603
Bangaren siyasa da zamantakewa:tawagar da ta kumshi yan majalisar dokokin kasar Labanon sun isa birnin Abu Zabin fadar mulkin hadeddiyar daular larabawa domin halartar taron majalisun dokokin kasashen musulmi karo na sha uku da za a gudanar a kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta almarkazia ya watsa rahoton cewa; tawagar da ta kumshi yan majalisar dokokin kasar Labanon sun isa birnin Abu Zabin fadar mulkin hadeddiyar daular larabawa domin halartar taron majalisun dokokin kasashen musulmi karo na sha uku da za a gudanar a kasar.Wannan taron na majalisun dokokin kasashen musulmi karo na sha uku da za a kwashe kwanaki hudu cir a jeri ana gudanarwa an fara gudanar da shi ne a ranar ashirin da takwas ga watan dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ajazirar Yas da ke gab da birnin na Abu Zabin.

732883

captcha