IQNA

An Guga Tare Da Yada Littafin Fikihun Musulunci A Mahanga Ta Duniya

20:03 - January 22, 2011
Lambar Labari: 2068778
Bangaren kasa da kasa, An buga tare da yada littafin fikihun musulunci a mahanga ta musulmin duniya baki daya, wanda babbar cibiya habbaka ayyukan al’adu muslunci ta kasa da kasa da dauki nauyin aiwatarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na ISESCO an bayyan acewa, an buga tare da yada littafin fikihun musulunci a mahanga ta musulmin duniya baki daya, wanda babbar cibiya habbaka ayyukan al’adu muslunci ta kasa da kasa da dauki nauyin aiwatarwa, da nufin yada mahangar musulmin ta bai daya kan lamarin shari’a a addinin muslunci.
Wannan littafi dai an buga shi ne a cikin harshen larabci, duk kuwa da cewa litatfan da aka nakalto bayanan da aka dogara da sua cikinsa mafi yawansu littafai da aka rubuta a cikin harshen larabci, yanzu haka dai an bayar da littafin domin saka shi cikin yanar gizo ta yadda masu bincike za su iya samunsa cikin sauki ta wannann hanya domin samun saukin bincike.
Bugawa tare da yada littafin fikihun musulunci a mahanga ta musulmin duniya baki daya, wanda babbar cibiya habbaka ayyukan al’adu muslunci ta kasa da kasa da dauki nauyin aiwatarwa, zai taimaka ma masu gudanar da bincike a jami’oin kasashen musulmi har ma da na turai kan matsayin shara a mahangar addinin muslunci.
734244



captcha