IQNA

10:13 - January 23, 2011
Lambar Labari: 2068968
Bangaren kasa da kasa, masu koyon karatun kur'ani mai tsarki a kasar Ghana na fuskatar matsalar karancin malamai da suka iya magana da harshen larabci, bisa la'akari da cewa an safkar da littafin mai tsarki ne cikin harshen larabci.Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada wakilansa da kuma daya daga cikin masu karatun kur'ani daga kasar Ghana da ya halarci gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Mashhad ya bayyana cewa, masu koyon karatun kur'ani mai tsarki a kasar Ghana na fuskatar matsalar karancin malamai da suka iya magana da harshen larabci, bisa la'akari da cewa an safkar da littafin mai tsarki ne cikin harshen larabci, kuma ilmominsa da dama a cikin harshen ne aka yi bayaninsu.

Usman Abdullah Yati wanda shi neya wakilci kasar Ghana a wannan gasa ya bayyana cewa, akwai dubban dalibai da suke da sha'awar koyon karatun kur'ani mai tsarki a kasar ta Ghana, akan haka yana kira ga kasashen musulmi da su taka rawa wajen kara bunkasa harkar karatun kur'ani a kasar, ta hanyar bude cibiyoyin kur'ani.

Ya ce ko shakka babu masu koyon karatu a kasar Ghana na fuskatar matsalar karancin malamai da suka iya magana da harshen larabci, bisa la'akari da cewa an safkar da littafin mai tsarki cikin harshen larabci ne.

733753

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: