Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani zaman taro a mtsayi na kasa da kasa domin nuna cikakken goyon baya fursunoni palastinawa da suke tsare a gidajen kason haramtacciyar kasar Isra'ila, wanda aka fara gudanarwa a birnin Ribat fadar mulkin kasar ta Morocco.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanr gizo na map.ma cewa, an fara gudanar da wani zaman taro a mtsayi na kasa da kasa domin nuna cikakken goyon baya fursunoni palastinawa da suke tsare a gidajen kason haramtacciyar kasar Isra'ila, wanda aka fara gudanarwa a birnin Ribat fadar mulkin kasar wadda daya ce daga cikin kasashen larabawan arewacin nahiyar Afirka.
An fara gudanar da zaman taron ne tare da halartar masana da kuma malaman jami'a na kasar, da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa, da ma wasu daga cikin kasashen yammacin turai, wadanda suke nuna matukar damuwa da halin da palastinawa suke ciki a gidajen kason Isra'ila.
Fara gudanar da zaman taro a mtsayi na kasa da kasa domin nuna cikakken goyon baya fursunoni palastinawa da suke tsare a gidajen kason haramtacciyar kasar Isra'ila, wanda aka fara gudanarwa a birnin Ribat, zai kara tabbatar wa duniya matsayin musulmi kan zaluncin Isra'ila a kan palastinawa.
734529