Bangaren siyasa da zamantakewa: Ayatullahi Abdul Amir Kablan mataimakin shugaban majalisar koli ta musulmi yan shi'ar kasar Labanon sakamakon tsananin rikicin cikin gida a kasar Masar ya bukaci kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ta gudanar da taron gaggawa na kokarin samar dab akin zaren kawo karshen wannan lamarin.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna ne ya watsa rahoton cewa; Ayatullahi Abdul Amir Kablan mataimakin shugaban majalisar koli ta musulmi yan shi'ar kasar Labanon sakamakon tsananin rikicin cikin gida a kasar Masar ya bukaci kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ta gudanar da taron gaggawa na kokarin samar dab akin zaren kawo karshen wannan lamarin. A ranar goma ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya mukaddashin shugaban na majalisar koli ta musulmin yan shi'ar kasar ta Labanon ya bukaci gudanar da taron gaggawa.
739524