IQNA

Taro Kan Juyin Musulunci Mai Taken Siyasar Waje Da Ta Cikin Gida

20:32 - February 02, 2011
Lambar Labari: 2074471
Bangaren siyasa da zamantakewa, A daidai lokacin da ake shirin fara gudanar da bukukuwan murnar tunawa da zagayowar lokacin juyin juya halin Musulunci a jamhuriyar ta Iran, za agudanar da wani zaman taro mai taken juyin muslunci da siyasar waje da ta cikin gida a birnin Moscow.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labar da ya nakalt daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilomin muslunci ta kasar an bayyana cewa, a daidai lokacin da ake shirin fara gudanar da bukukuwan murnar tunawa da zagayowar lokacin juyin juya halin Musulunci a jamhuriyar ta Iran, za agudanar da wani zaman taro mai taken juyin muslunci da siyasar waje da ta cikin gida a birnin Moscow fadar mulkin kasar Rasha.

Karamin ofishin jakadancin jamhuryar Musulunci ta Iran da ke birnin Moscow shi ne zai dauki nauyin gudanar da wannan zaman taro, tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar Rasha kamar yadda ya saba gudanarwa a kowace shekara a irin wannan lokaci.

Kasar dai na daya daga cikin kasashen suke da kyakkyawar danganataka da Iran ta fuskacin raya ala;dun bangarorin biyu, bisa la'akari da tsawon tarihin makwaftaka da suke da shi, wanda hakan shi ne babban gishikin alakarsu.

739404




captcha