Bangaren kasa da kasa, A cikin mako mai zuwa ne za afara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa a tarayyar Nigeria, wadda jahar Jigawa da ke arewacin kasar za ta dauki bakuncinta, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassan kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Tribune an bayyana cewa, a cikin mako mai zuwa ne za afara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa a tarayyar Nigeria, wadda jahar Jigawa da ke arewacin kasar za ta dauki bakuncinta, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassan kasar, musamman ma daga arewaci inda mabiya addinin musulunci suka rinjaye.
Shugaban kwamitin kula da harkokin kur’ani na jahar Jigawa Haruna Wakili, ya sheda cewa wannan gasar karatun kur’ani za ta samu halartar makaranta daga jahohi 30 na kasar, adadin makarnatanb kuma zai kai mutane 550, tare da halartar baki da yawansu zai kai mutane 1000 a kalla.
Ya kara da cewa jahar Jigawa na daga cikin jahohin Nigeria da suke mayar da hankali wajen bunkasa harkokin addinin musulunci da kuma ilimi, bisa la’akari da cewa jaha ce ta mabiya addinin musulunci, kuma acewarsa za su ci gaba da shirya irin wadannan taruka na gasar kur’ani.
Wannan dai shi ne karo na ashirin da biyar da za agudanar da wannan gasa a matsayi na kasa a tarayyar Nigeria, amma kuma shi ne karon farko da jahar Jigawa za ta dauki bakuncinta.
741439