Bangaren kasa da kasa, Ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Kuwait ta sanar cewa za afara yin afuwa ga mutanen da suke tsare a gidan kaso sakamakon aikata wasu laifuka, amma wadanda suka hardace kur’ani mai tsarki daga cikinsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Gulfnews cewa, ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Kuwait ta sanar cewa za afara yin afuwa ga mutanen da suke tsare a gidan kaso sakamakon aikata wasu laifuka, amma wadanda suka hardace kur’ani mai tsarki daga cikinsu da suke tsare.
Bayanin ya ci gaba da cewa akwai wasu daga abubuwan da za a yi la’akari da su kafin fayyace wadanda suka canci shiga cikin wannan afuwa ta gwamnati, daga ciki kuwa har kula lamarin addini, da kyawawan dabi’u da kuma tin tilawar kur’ani mai tsarki tare da kiyaye ka’idoji na addini.
Ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Kuwait ta sanar cewa za afara yin afuwa ga mutanen da suke tsare a gidan kaso sakamakon aikata wasu laifuka, amma wadanda suka hardace kur’ani mai tsarki daga cikinsu a gidan kason.
741415