Bangaren kasa da kasa, Ministoci a ma’aikatun kula da harkokin kanan yara na kasashen musulmi 22 ne za su halarci zaman taro na musamman da aka shirya a karo na uku a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO an bayyana cewa, ministoci a ma’aikatun kula da harkokin kanan yara na kasashen musulmi 22 ne za su halarci zaman taro na musamman da aka shirya a karo na uku a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libya domin yin dubi kan yanayin kanan yara suke ciki a kasashen musulmi, da kuma taimakon da suke bukata.
Wannan zaman taro dai cibiyar raya al’adu da ilmomin musulunci ta ISESCO ce ta dauki nauyin shirya shi tare da gudanar da shi, tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da ayyukan addinin muslunci ta kasar Libya, kamar yadda ta dauki nauyin shirya wasu makamantansa biyu a lokutan baya.
Ministoci a ma’aikatun kula da harkokin kanan yara na kasashen musulmi 22 ne za su halarci zaman taro na musamman da aka shirya a karo na uku a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libya da aka fara gudanar da irinsa tun shekaru biyu da suka gabata.
741365