Bangaren kasa da kasa, Babban kwamitin kula da harkokin bankuna na kasar India da ke da rassa daban-daban a kasashen duniya, ya shirya gudanar da wani zaman taro kan harkokin kudi bisa tsari na bankunan musulunci, wanda aka gudanar a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Gulf Times an habarta cewa, babban kwamitin kula da harkokin bankuna na kasar India da ke da rassa daban-daban a kasashen duniya, ya shirya gudanar da wani zaman taro kan harkokin kudi bisa tsari na bankunan musulunci, wanda aka gudanar a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar a reshensa dake kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a yayain zaman taron wanda ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen Asia da kuma kasashen turai, an tattauna irin rawar da bankin musulunci yake takawa a dukkan lamurra da suka danganci harkokin kudi a matsayi na kasa da kasa, da kuma yadda sauran cibiyoyi za su iya yin koyi da salon bankin muslunci a harkokinsu.
Kwamitin kula da harkokin bankuna na kasar India da ke da rassa daban-daban a kasashen duniya, ya shirya gudanar da wani zaman taro kan harkokin kudi bisa tsari na bankunan musulunci, wanda aka gudanar a birnin Doha.
744083