IQNA

Ana Shirin Gudanar Da Zama Na Amincewa Da Addinin Muslunci A Spain

21:37 - February 12, 2011
Lambar Labari: 2079649
Bangaren kasa da kasa, Ana shirin gudanar da wani zaman taro da zai yi kan matsayin addinin muslunci da kuma amincewa da shi a matsayin daya daga cikin addinan kasa a Spain, wanda za a gudanar a birnin Madrid fadar mulkin kasar, tare da halaratr masana daga sassa daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran MAP na kasar Morocco an bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro da zai yi kan matsayin addinin muslunci da kuma amincewa da shi a matsayin daya daga cikin addinan kasa a Spain, wanda za a gudanar a birnin Madrid fadar mulkin kasar, tare da halaratr masana daga sassa daban-daban na kasar ta Spain.
Taron za a gudanar da shi domin duba matsayin addinin muslunci da kuma irin karbuwar da yake samu tsakanin al’ummar kasar, gami da karuwar mabiya addinin musulunci, wanda hakan ya sanya masana fara yin tunani kan tattauna batun amincewa da addinin muslunci a hukumance a kasar.
Yanzu haka dai ana shirin gudanar da wani zaman taro da zai yi kan matsayin addinin muslunci da kuma amincewa da shi a matsayin daya daga cikin addinan kasa a Spain, wanda za a gudanar a birnin Madrid fadar mulkin kasar, tare da halaratr masana daga sassa na kasar.
745743


captcha