IQNA

An Bude Wata Sabuwar Cibiyar Harkokin Musulunci A Strasburg

21:38 - February 12, 2011
Lambar Labari: 2079651
Bangaren kasa da kasa, An bude wata sabuwar cibiyar addinin muslunci a birnin Strasburg na kasar Faransa tare da halartar Oliver Bitzmataimakin magajin garin birnin, da kuma wakilan kungiyoyin mabiya addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Oumma ya habarta cewa, an bude wata sabuwar cibiyar addinin muslunci a birnin Strasburg na kasar Faransa tare da halartar Oliver Bitzmataimakin magajin garin birnin, da kuma wakilan kungiyoyin mabiya addinin musulunci na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa cibiya ta hada dakin karatu da kuma babban masallaci da wuraren gudanar da taruka, a lokacin yake gabatar da bayani, mataimakin magajin garin birnin ya bayyana cewa, bayan wannan aiki, an kuma samar da makabarta da ta kebanci mabiya addinin musulunci da yankin.
An bude wata sabuwar cibiyar addinin muslunci a birnin Strasburg na kasar Faransa tare da halartar Oliver Bitzmataimakin magajin garin birnin, da kuma wakilan kungiyoyin mabiya addinin musulunci.
745362



captcha