Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama cewa, za a gudanar da wani zaman taro na samar da hadin gwiwa tsakanin dukkanin addinai na duniya wanda za a gudanar a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia domin samar da hadin gwiwa tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Taron zai mayar da hankali ne wajen gabatar da muhimman shawarwari na samun fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya, da kuma yadda za su iya yin aiki kafada da kafada ba tare tauye wa wani bangare hakkinsaba, haka nan kuma tare da girmama ra'ayi da mahangar juna.
Gudanar da wani zaman taro na samar da hadin gwiwa tsakanin dukkanin addinai na duniya wanda za a gudanar a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia wanda shi ne irin na uku da za a gudanar yada matukar muhimmanci ga mabiya addinai na duniya.
746789