IQNA

An Fara Gudanar Da Shirin Bayar Da Horon Hardar Kur'ani A Birnin Riyad

12:43 - February 19, 2011
Lambar Labari: 2083163
Bangaren kas ada kasa, An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a birnin Riyad fadar mulkin kasar saudiyya, wanda ya kebanci kananan yara da mahaifansu ke butar su samu horon hardar kur'ani mai tsarki tun daga kuruciyarsu.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Aljazeera an bayyana cewa, an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a birnin Riyad fadar mulkin kasar saudiyya, wanda ya kebanci kananan yara da mahaifansu ke butar su samu horon hardar kur'ani mai tsarki tun daga kuruciyarsu domin samun harda mai inganci..

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai da dama daga cikin masu sha'awar shiga cikin wannan shiri, amma an riga an kayyade shirin ga kanan yara 'yan kasa da shekaru goma, kuma yanzu haka daruruwan yara ne suka sammun wannan horo wanda zai dauki wasu 'yan lokuta ana gudanar da shi.

Ma'aikatar kula da harkokin addinin ta kasar saudiyya tare da hadin gwiwa da cibiyar raya harkokin kur'ani a kasar saudiyya sun e suke daukar nauyin gudanar da wannan shiri, kamar yadda kakakin ma'aikatar ya sheda wa manema labarai.

An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a birnin Riyad fadar mulkin kasar saudiyya, wanda ya kebanci kananan yara da mahaifansu ke butar su samu horon hardar kur'ani mai tsarki.

Za a gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka yi lakabi da gasar Alsawi ta za ta kebanci nakasassu a birnin Sharja na kasar hadaddiyar daular larabawa. 749737

captcha