Bangaren kasa da kasa, Daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci na kasar India Maulana Furqan Kasimi ya sheda cewa, juyin juya halin Musulunci an kasar Iran ya samu karbuwa a wajen musulmi a fadin duniya, kasantuwarsa wani babban sako na addininsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkausar an bayyana cewa, daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci na kasar India Maulana Furqan Kasimi ya sheda cewa, juyin juya halin Musulunci an kasar Iran ya samu karbuwa a wajen musulmi a fadin duniya, kasantuwarsa wani babban sako na addini da dukkanin musulmi suke amfana da shi..
Bayanin ya ci gaba da cewa malamin wanda ya shahara ta fuskacin kira zuwa ga addinin muslunci da kuma fahimtar manufarsa, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban dubban daruruwan mutane da suka taru taron cibiyar yada al'adun Musulunci da ke birnin New Delhi na kasar India.
Ya ci gaba da cewa a koda yaushe makiya Musulunci suna daukar matakan murkushe addinin muslunci, bayan da suka lura cewa shi ne addinin da ke 'yantar da dan adam daga bautar bayi, kuma babban misalin hakan a wannan zamani da muke rayuwa shi ne abin da ya faru a kasar Iran.
Babban malaman addinin musluncin na kasar India Maulana Furqan Kasimi ya sheda cewa, juyin juya halin Musulunci an kasar Iran ya samu karbuwa a wajen musulmi a fadin duniya, kasantuwarsa wani babban sako na addininsu.
749836